Fadar Beijing ta sha alwashin daukar matakai daidai da wadanda Amurka ta dauka na sanya mata takunkumi,.
Wannan zazzafan martanin na Chaina ya biyo bayan matakin da Amurkan ta dauka ne na bai wa Hong Kong damar kasancewa zama yanki mai cin gashin kanta kamar kasar ta Chana.
A ranar Talata ne Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta ba shi damar aiwatar da wannan hukuncin domin ganin birnin Hong Kong ya koma kasa mai zaman kanta.
Wannan sabon rikicin kamar yadda rahotanni suka tabbatar, ya biyo bayan dokar tsaron da Chana ta kakaba ne a yankin na Hong Kong, inda dokar ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifi, bayan majalisar dokokin Chana ta kada kuri’ar amincewa da ita, tare da bai wa kotun Chana damar zartar da hukunci ga wadanda aka kama da aikata munanan laifuka da suka saba dokar a yankin Hong Kong.