Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi a ranar Lahadi sun tabbatar da mutuwar mutum takwas a Ukwagba da Mgbo, dake karamar hukumar Ohaukwu a jihar sakamakon harin da wadansu suka kawo daga Agila dake Binuwe. Sai dai hukumomin sun dora alhakin wannan rikicin akan masu ruwa da tsakin na yankunan.
DSP Loveth Odah, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ta shaidawa manema labarai cewa; lamarin ya auku ne a ranar Asabar. Inda hudu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sare musu wuya aka yi.
Sai dai ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Awosola Awotinde, da kuma wadansu manyan jami’an ‘yan sanda da shugaban karamar hukumar Ohaukwu sun je wurin da lamarin ya auku. ‘Yan sandan sun je mutanen kauyen sun shaida musu cewa daga Agila a cikin jihar Binuwe wadansu mutanen suka zo suka same su suka kawo musu hari, inda suka kona gidaje shida da kashe dabbobi guda ashirin.
Kakakin ‘yan sanda ta ce daga cikin wadanda aka fillewa wuya sun hada da; James Aleke, 55, Innocent Agbo, 65, Chukwu Enwe, 46, da kuma Livinus Idoko, 70. Ya ce wadanda kuma kashe su kawai aka yi ba a fille musu wuya ba sun hada da; Ngozi Idenyi, 32, Jonathan Onwe, 10, Ify Aleke, 51, da Susanna Ogba, 54, yayin da Okeh Nwankwo, 53, yana jinya a asibiti.
Kwamishinan ‘yan sandan ta gargadi mutanen kauyen da kai harin ramuwar gayya. Ta ce; zai tabbatar da an kawo zaman lafiya a yankin. Inda Odah ya shawarci gwamnatin tarayya da ta shiga lamarin.