Aƙalla mutane 31 da suka haɗa da yara ƙanana ne aka kashe a cikin makon da ya gabata a wani sabon rikici daya barke a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kazamin fada tsakanin sojojin Congo da kungiyoyin ‘yan tawaye da dama ya bazu zuwa yankin Beni inda aka gano gawarwaki biyar a ranar Laraba.
Mazauna yankin sun ce kila adadin wadanda suka mutu ya zarce haka yayin da mutane da dama suka bace.
Rahotanni sun nuna cewa, sama da mutane 700,000 ne suka tsere daga gidajensu a lardin Ituri da arewacin Kivu tun farkon wannan shekarar.
Wannan dai ya kawo adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa miliyan shida sakamakon rikicin masu dauke da makamai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce yana cikin mafi munin rikicin a duniya.
Sojojin Congo na fafatawa da gungun ‘yan tawaye da dama a gabashin kasar.
Kazalika da yawa daga cikinsu sun ajiye makamansu tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar a shekara ta 2003 amma a baya-bayan nan sun sake kunno kai.
A wani labarin Kuma na Daban.
Kansilolin PDP sun koka kan yawaitar kashe-kashe a Kudancin Kaduna
Kansilolin Jam’iyyar PDP daga yankin Kudancin Kaduna sun koka kan yawaitar hare-hare akan Al’ummomin su da ƴan ta’adda suke cigaba da yi.
Wannan na zuwanm ne a yayinda Kansilolin suka yanke hukuncin cewa Ɗan Takarar Sanata a yankin na Shekarar 2023, Barister Sunday Marshall Katung yana da hadin yadda za tabbatar da samun tsaro a yankin.
Da yake jawabi a lokacin taron Manema Labaru a ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Kansilolin Hon. Obed Danjuma Gankon yace yankin Kudancin Kaduna, kamar sauran yankuna a Jahar, yana fama da matsalar ƴan Ta’adda.
“Wannan ƴan ta’addan sun tada al’ummatai, sun yiwa mata fyaɗe, sun kashe tare da sace mutane, ciki har da yara. Sun lalata Al’ummomi, sun yara ba tare da gidaje ba,” Inji shi.
Gankon wanda yana tare da dukkanin Kansilolin PDP da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin Kaduna ta Kudu, yace sun amince Katung ya wakilce su a Shiyyar.