Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji masu juyin mulki a ƙasar Mali sun tsare Shugaba Ibrahim Boubakar Keïta bayan ƙwace iko a ƙasar.
Wani kakakin gwamnatin ƙasar ya ce sojojin da suka yi ta harbe-harbe sun kuma yi awon gaba da Firaminista Boubou Cissé duk da cewa a baya ya yi kira da a yi tattaunawa ta fahimta.
Yunƙurin juyin mulkin ya fara ne a safiyar Talata inda sojojin suka yi ta harbe-harbe a wani sansani a garin Kati da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.
A ranar Talatar ne kuma gungun wasu matasa masu zanga-zanga suka cinna wa gine-ginen gwamnati wuta a yayin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Bamako.
Gabanin nan sojoji sun tayar da tarzoma a babban barikin na Kati inda suka kame tare da kukkulle manyan hafsoshi a kwamandojinsu suka ƙwace iko.
Tuni dai Tarayyar Afrika da Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da ƙasar Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka suka la’anci juyin mulkin.
Matakin da sojojin ƙasar suka ɗauka ya zo ne a yayin da ake ta gangamin gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Keita ya yi murabus.
‘Yan ƙasar na zargin shugaban da gaza magance matsalar tsaro da durƙushewar tattalin arziki baya ga yawaitar cin hanci da rashawa da ake zarginsa da shi.