Kotun koli ta yi watsi da karar da Hon. Suleiman Alhassan Gwagwa ya Kai gabanta, inda yake kalubalantar Hon. Murtala Karshi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a karamar hukumar Abuja Munincipal (AMAC) a zaben kananan hukumomin FCT dake tafe.
Karshi ya garzaya kotun koli domin abukatar ” yin adalci” inda yake kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta bayyana Gwagwa a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben ranar 12 ga watan Fabrairu shekarar 2022.
Lokacin da yake yanke hukuncin Alkalin kotun Mai shari’a Chima Centus Nweze JSC. ya bayyana cewa duk hujjojin da wanda ake kara ya gabatar na kalubalantar takarar Karshi ba su da inganci.
Kuma Nan take yayi washi da karar, saboda rashin “cancanta”, yayin da ya ayyanai Murtal Karshi a matsayin halattaccen Dan takara.
Murtala Karshi yayin da yake magana kan hukuncin, ya yabawa kotun kolin da ta kawo karshen cece-kucen da ake ta tafkawa a tsakanin su.
Ya yi kira ga daukacin magoya bayan jam’iyyar APC da su zama tsintaiya madaurinki daya, domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu kujerun shugabanni kananan Hukumomi da kansiloli a Babban Birnin Tarayya Abuja, yana mai kira ga duk wanda ya samu matsala da shi, da suzo a hada kai don ganin jam’iyyar ta samu nasara.