Ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a Jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.
Shugaban Tsagin, Ahmadu Haruna Zago, ƙarƙashin jagorancin Tsohon Gwamnan Jahar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya shaidawa sashen BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 5 Sun Jikkata Yayin Wata Gobara A Jihar Legas
“Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban,” in ji shi.
“Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun,” in ji Ɗanzago.
A cewar Majiyar mu ta Daily Nigerian, Sashen Hausa na BBC ta ruwaito cewa hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.
A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.
A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam’iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.