Rikicin Atiku da Wike rashin Fahimta ce kurum — Jigon PDP
Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin, ya gargadi ‘ya’yanta da ma daukacin ‘yan Nijeriya da su guji haifar da munanan ƙin jini da rudani tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a gabanin babban zaben 2023.
Jigon na PDP ya lura cewa rikicin da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa da Wike bai kamata a ware shi a matsayin matsala ba sai dai kawai “rashin fahimta” a cikin jam’iyyar.
Wannan a cewarsa bai wuce yadda jam’iyyar ta zage damtse ba domin kokarin sasanta Atiku da Wike.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tallafin Man Fetur Na Laƙume Naira Biliyan 18.39 A Kullum – Minista
Don haka ya roki ‘yan Jam’iyyar da su mika goyan bayansu ga kwamitin sulhu da jam’iyyar ta kafa domin sasanta rikicin.
Jigon PDP ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da jaridar PUNCH ta samu a Kaduna ranar Alhamis.
Jibrin, Sanata a Jamhuriya ta biyu, ya kuma gargadi ‘yan jam’iyyar da su kara maida hankali wajen ganin sun ci zabe a 2023.
Ya ce, “Ina so in yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar PDP da daukacin ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, kada su haifar da ƙin jini da rudani a cikin halin da jam’iyyarmu ke ciki, lura da cewa, duk kokarin da ake yi na sasantawa tsakanin Wike da Atiku.
“Abin da ke faruwa a yanzu bai kamata a ware shi a matsayin matsala ba illa rashin fahimtar juna a cikin jam’iyyar.
“Shawarata mai karfi ita ce mu ba da kwakkwaran goyon baya ga kwamitin sulhu na yanzu da aka kafa domin warware dukkan batutuwa.
“A wannan lokacin da zai kai ga zaben 2023 ya kamata mu mai da hankali kan yadda za mu samu nasara a dukkan mukamai da za a yi takara tare da bin ka’idoji.