Gawar wani mutum da aka binne a Akwa Ibom an ƙwaƙulo ta, sakamakon wani rikici na duniya, inda aka jefar da akwatin gawar a wani wuri a cikin yankin.
Haka zalika, an kai gawar a wuraren ajiye gawa, a yayinda ƴan sanda ke cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.
Mamacin mai suna Aniefiok Bassey mai shekaru 61, ya rasu a ranar 23 ga watan Yulin shekarar 2021, an binne shi a ranar 25 ga watan Satumba, bayan an gudanar al’adu ciki har da ibada a coci, amma an tono gawar sa, awanni kaɗan bayan binne shi, al’amarin daya jefa mutanen yankin cikin tsoro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Basaraken Gargajiya a Taraba, ya rasu a Fadarsa
Lamarin ya faru a Al’ummar Usung Itiat na Ƙaramar Hukumar OrukAnam ta Jihar Akwa Ibom.
Uduak Bassey, ɗan uwan mamacin, yace a cikin wani ƙorafi daya shigar ga ƴan sanda cewa al’amarin cin mutunci ne da wulaƙanci, da ka’iya haifar da faɗace-faɗace a cikin al’umma.
Mr Bassey ya shaidawa ƴan sanda cewa shugaban ƙaramar hukumar ƙauyen Usung Atiat Aniedu Thompson shine ya ciro gawar, sabudda iyalan wanda ya mutu, basu bayar da kayayyakin da ya buƙata ba, domin cika wasu sharuɗɗa na Al’ada.
Yace awaki, da doya guda biyar, da jarkar man ja, na daga cikin kayayyakin da shugaban ƙauyen ya buƙata.
A lokacin da aka tuntuɓi Shugaban Ƙauyen, Mr Thompson ya tabbatar dacewa ya buƙaci a bashi kayayyakin a madadin ƙauyen, inda yace wanda ya mutu yana ɗaya daga cikin mutanen da suka yi wannan dokar, da a halin yanzu take shafar iyalan sa.
Mr Thompson yayi zargin cewa, wanda ya rasu ya zubawa matar wani guba a lokacin yana raye, inda aka kore shi daga ƙauyen.
Amma ya musanta batun shi ya tono gawar, wanda yace an tono gawar ne sabudda an sanya shi a wani wuri wanda bai dace ba.
Mfon Sunday, mazaunin kusa da al’ummar Nung Oku Ubo 1 yace shine ya tono gawar sabudda an binne ta a ƙasar shi.
Mr Sunday Wanda ya bayyana cewar a shirye yake yayi yaƙi da duk wanda zai shigo a ƙasar.
Silas Akifa, ɗaya daga cikin iyalan shi ta tabbatar dacewa akwai rigingimu sabudda cin iyaka, amma kotu ta yanke hukunci a madadin wanda ya mutu a shekarar data gabata.