Wata babbar kotun jihar Kano dake zaman ta a Miller Road ƙarƙashin jagorancin mai sharia Ibrahim Musa Karaye, ta ɗage ci gaba da sauraran shari’ar da ake yi ga matar nan da ake zargi da yanka ɗanta, har zuwa ranar huɗu ga watan gobe na Oktoba.
Matar da ake zargi da aikata laifin mai suna Saratu Ya’u mazauniyar garin Sabon birni a yankin ƙaramar hukumar Gwarzo, tun a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2018 aka gurfanar da ita gaban kotun ana tuhumarta da laifin yanka ɗan nata mai suna Buhari Abubakar mai shekaru biyar a duniya.
Lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soron Dinki ya nemi izinin kotu domin a karanta mata laifin da ake zarginta da aikatawa, wanda ba tare da bata lokaci ba ta amince da aikata laifin yanka yaron nata.
Sai dai bayan tashi daga zaman kotun, Alƙalin kotun ya bada umarnin kaita asibiti domin duba lafiyar ƙwaƙwalwarta.