By Abbas Yakubu Yaura
Kwamandan (OPSH), Manjo Janar Ibrahim Ali ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin Kwamitin mutum 36 da ya kaddamar kwanan nan don tsara hanyoyin da za a bi don samun dawwamammen zaman lafiya a Filato da kewaye ta.
Ya sanar da hakan ne a ranar Asabar 23 ga watan Oktoba 2021 a wani biki da aka shirya don karbar rahoton kwamitin a hedkwatar jami’an tsaron dake birnin Jos. Kwamandan ya bayyana cewa rahoton zai taimaka musu, tare da gwamnatin jihar Filato da sauran hukumomin tsaro wajen cimma nasarar samum zaman lafiya a kan tudu.
Sannan ya kara da cewa OPSH dake ƙarƙashin umurninsa ta haɓaka ingantattun dabaru waɗanda ba na asali ba waɗanda aka tsara don kawo ƙarshen tashin hankali da haɓaka zaman lafiya tsakanin mutanen da ke zaune a jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Manjo Janar Ibrahim Ali yace kwamitin ya fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki na al’ummomin da aka yi niyya don samar da rahoton aikin.
Ya bayyana cewa rahoton zai zama ginshikin samara da dawwamammen zaman lafiya da jama’a ke iƙirari da shi.Ya gode wa kwamitin na mutum 36 da suka yarda su yi aiki tare dashi da kuma jajircewarsu kan aikin.
A cikin sakon fatan alheri ga ma halatta taron, Barista Ngwe Rigwe da Shugaban Majalisar Gargajiya ta Bassa,da Rev Ronku Aka mai ritaya, Da Gwom Rwei na Jos ta Kudu, Dakta Nga Dangyang da Ardo Wada Waziri na Miyango sun yaba wa OPSH saboda kyakkyawan ƙoƙarin ta na kawo zaman lafiya jihar.
Shi ma da yake magana, wakilin Darakta Janar na Hukumar Gina Zaman Lafiya ta Jihar Filato, Mista Gayi Timothy Gayi ya bayyana Kwamitin a matsayin mai cike da wakilai daga dukkan kungiyoyin kabilu.