A ƙoƙarin samo bakin zaren warware wannan rikici babban sufeton ‘yan sandan ƙasar nan Muhammad Abubakar Adamu, ya jagoranci zaman tattanawa tsakanim ɓangarorin biyu.
Ɓangarorin dake gaba da juna a yankin Zuru sun haɗa da Fulani da Dakarkari, inda kowanne ɓangare ke zargin ɗaya ɓangaren da yin kisan gilla ga mutanensa, ba tare da an hukunta mai laifi ba.
Zaman da babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya ya jagoranta, ya samar da dama ga kowanne ɓangare ya faɗi ƙorafe-korafensa da manufar hanyar da za a samar da zaman lafiya.
https://dimokuradiyya.com.ng/rashin-tsaro-a-kasashen-yarabawa-an-tsaurara-tsaro-a-yankin/
Da yake bayyana dalilin kiran wannan taro, shugaban ‘yan Sandan ya ce, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya damu da halin da yankin Zuru yake ciki, shiya sa ya aika shi domin zama da dukkan ɓangarorin domin nemo hanyar gyara.
Wasu mazauna yankin daga ɓangarorin biyu sun bayyana halin da wannan yanki ke ciki, inda kowanne ɓangare ke ɗora laifi akan ɗaya ɓangaren.