Rikicin Hijabi: Musulman Kwara sun yi Allah wadai na kasawar Gwamnati wajen biyan Diyyar rai
Musulman Jahar Kwara a Ƙananan Hukumomin Offa da Oyun a ranar Alhamis sun yi kira ga Gwamnatin Jahar data saki takardar akan rahoton kwamitin data kafa domin ya tabbatar da Rikici kan sanya Hijabi da Ɗalibai mata a Makarantar Oyun Baptist, Ijagbo.
Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewar a ranar 3 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022, wani rikici ya ɓarke kan amfani da Hijabi daya haddasa kisan mutum ɗaya tare da Jikkata Mutane 10 ta hanyar harbin bindiga.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun samu nasarori a yaƙi da Matsalar Tsaro, yanzu haka zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa — Buhari
Gwamnati a satin daya gabata, ta sake buɗe Makarantar bayan ta samu rahoto akan Kwamitin data kafa yayi bincike, amma har yanzu bai kawo farar takarda kan rahoto.
Da yake jawabi a Ilori a taron Manema Labaru, masu ruwa da tsaki sun buƙaci gwamnatin jihar data tabbatar an kamo wanda suka yi kisan tare da zartar Masu Da hukunci.
Mai Magana da Yawun Musulman Mohammed Nuruddeen Yace “,Masu ruwa da tsaki na kira ga Gwamnati data saki rahoton kwamitin data kafa kan rikicin Hijabi.
Masu ruwa da tsaki sun yi Allah wadai akan shigar da gwamnati tayi akan rikicin.
Sun kuma yi Allah wadai kan bada kuɗin da Gwamnati tayi, da suka ayyana shi a matsayin Ɗan Kaɗan ga iyalan wanda ya mutu a matsayin diyya, da kuma wanda suka ji raunuka.
Comments 1