Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kan mukamin shugabancin Jam’iyar APC ba kamar yadda shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC mai mulki, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamna Sani Bello na Jihar Neja ya shiga ofishin shugaban riko a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin da wasu da dama suka bayyana a matsayin sabon rikicin da ya barke a jam’iyyar APC.
Da yake magana a gidan talabijin na Channels cikin wani shir Mai taken Politics Today, El-Rufa’i ya ce Buni, wanda a halin yanzu baya kasar nan, zai iya komawa a matsayinsa na gwamnan jihar Yobe ne kadai amma ba a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ba.
Ya ce Bello yana samu goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni jam’iyar APC 19.
“Buni ya tafi, sakataren ya tafi. Gwamna Bello ne ke kan mulki kuma yana samun goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 19. Buni ba zai iya dawowa matsayinshi a APC ba, Amma zai iya Komawa kan matsayinsa na gwamnan Yobe, amma ba zai taba zama shugaban jam’iyyar mu ba.” Inji El-Rufa’i
“Shugaba Buhari ya bada umarnin tsige shi kuma an aiwatar da hakan. Gwamna Bello ya karbi mulki kuma abubuwa suna tafiya bisa tsari. ”
“Za a maido da jam’iyya kamar yadda take da, Kuma za a gudanar da babban taron kamar yadda aka tsara. Gwamnoni 19 da mataimakansu ne ke goyon bayan wannan matakin. Buni da mutanensa sun samu umarnin kotu na dakatar da taron amma sun boye.”
Comments 1