Rikici ya karade a cikin jam’iyyar PDP inda manyan jagorori bakwai suka ajiye makamansu. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Babban Sakataren jam’iyyar na Kasa Colonel Austin Akobundu (retd), ya sanar da ajiye aikinsa, cikakken bayani akan hakan na zuwa.
Shugaban jam’iyyar na Kasa Uche Secondus, yana fuskantar matsi daga mabiyansa kan ya ajiye mukaminsa, a yayinda wa’adin mulkinsa zai Kare ne a karshen watan December.
KARANTA:- Gamayyar Kasashen Larabawa (UAE) ta tsawaita dokar da ta sanyawa Nigeria na zirga-zirga
Rikicin ya kaiga har sai da suka sami sabani da mai tallafa masa Nyesom Wike, a gaban jama’a.
Sai dai gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom, yayi kokarin ya ga ya sasanta tsakaninsu amman abun yaci tura.
Kamin dai samun sabanin su da Wike, shugaban jam’iyyar PDP na Jahar Oyo Kassim Afegbua, ya kira ga Secondus, da ya sauka daga mukaminsa duba da yadda yakema jam’iyyar rikon sakainar Kashi.
Inda ya zarge shi da cin hanci, har takai ga ya makashi kotu.
Haka shima Secondus, ya makashi kotu saboda zarginsa na bata masa suna.
Idan baku manta ba gwamna David Umahi (Ebonyi), Ben Ayade (Cross River), da Bello Matawalle (Zamfara) inda sun rigada sun fice daga Jam’iyyar PDP zuwa (APC).
Wannan ya sanya dayawa daga cikin mabiya jam’iyyar ta PDP su fara zargin shugabancin Secondus.
Adai karshen watan July ne Dan majalisa Rimamnde Shawulu, ya kira ga Secondus din ya sauka.
Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, baice komai ba a lokacin da ake tattara wannan rahotan.