Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau wanda ke jagorantar wani bangare na jam’iyyar APC a Kano, ya ki amsa gayyatar ofishin sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali.
Platinum Post ta ruwaito cewa Mista Alkali ya gayyaci Shekarau ne tare da wasu ‘yan kungiyarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Daina Ganin Sa A Shirin Dadin Kowa Ina Sallau ya shiga Ne
Haka kuma an mika goron gayyata ga jiga-jigan jam’iyyar masu biyayya ga Gwamna Abdullahi Ganduje.
Wannan Jarida ta ruwaito bisa gaskiya cewa wadanda aka gayyata daga sansanin Ganduje sun karrama wannan gayyata tare da karbar bayanansu kuma ‘yan sanda sun bukaci su je.
Sai dai wata majiya mai tushe daga Louis Edet da ke Abuja ta shaida wa PlatinumPost cewa babu daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar ta Shekarau.
“A gaskiya zan iya gaya muku cewa ba su zo ba, ina maganar ’yan sansanin Shekarau ne amma dayan bangaren sun zo mun yi abin da ake bukata kuma sun tafi.