A jiya lahadi Kwamandan Operation Safe Haven OPSH, Manjo Janar Ibrahim Ali , ya kaddamar da kwamitin hadin gwiwa na zaman lafiya mai mambobi 36 don nemo hanyoyin magance hare-hare ramuwar gayya tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato.
An gudanar da taron ne a Shelkwatar rundunar soji dake Jos, Babban Birnin Jihar.
An kafa Kwamitin ne sakamakon rikice -rikicen baya -bayan nan a jihar, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da lalata dukiyoyin masu yawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda za ta binciki Kwakwalwar jami’in ta
Mambobin kwamitin sun fito ne daga kabilu daban -daban na kananan hukumomin Bassa, Jos ta Arewa da Jos Kudu, da akafi samun rikice-rikice, Wanda ake fatan abubuwan da suka tattauna za su taimaka wajen nemo mafita mai dorewa kan rikice -rikicen da ba su da tushe a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna. Da Kuma Dawo da dauwamammen kzaman lafiya a jihar.
Da yake jawabi a lokacin kaddamarwar, Manjo Janar Ali ya bukaci mambobin kwamitin da su nuna rashin son kai, domin tabbatar da samun zaman lafiya a jihar.
A nashi bangaren Shugaban kwamitin na zaman lafiya, Prince Robert Rigwe Ashi, yayin da yake gode wa kwamandan bisa amincewar da aka yi musu, ya ba da tabbacin cewa, kwamitin zai gudanar da ayyukan sa bisa gaskiya da kuma adalci.