By Abbas Yakubu Yaura
An tsinto gawar wani matashi da har yanzu ba a tantance ba a hanyar Essi Layout da ke karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta.
Shaidun gani da ido sun ce marigayin ya kasance wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne data tayar da hankali a yankin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an tsinci gawar mamacin ne a ranar Asabar kuma ana zargin an kashe shi ne cikin dare.
A cewar majiyoyi, an gano shi ne a cikin wani tafkin jini tare da saran adda a goshi da kuma hannayensa.
An tattaro cewa an jiyo karar harbe-harbe da dama dake tashi akan iska a cikin daren jiya yayin da wadanda ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suke fafatawa a tsakanin junan su.
Idan zaku iya tunawa rikicin kungiyar asiri tsakanin ‘yan kungiyar Vikings da Eiye a watan Disambar da ya gabata ya yi sanadin mutuwar mutum daya a cikin Iyara-Essi Layout na Warri.
Sai dai kuma wakilinmu ya kasa tantance ko rikicin daya sake afkuwa yana da alaka dana bara ne.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kazalika PPRO ya ce, “Rikicin kungiyar asiri ne.”