By Ishaq Dabai
Kwamishinan ‘yan sandan dake kula da rundunar’ yan sandan jihar Benue, Tunji Akingbola a ranar Alhamis yace rikicin manoma da makiyaya yana ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na jihar.
CP Akingbola ya bayyana cewa lamarin yaci gaba duk da kokarin da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki na al’umma.Da yake magana a wurin taron manema labarai na ‘yan jarida a ofishinsa, shugaban’ yan sandan na Benue ya lissafa kananan hukumomin da galibin rikicin manoma da makiyaya yafi shafar su da suka hada da Guma, Gwer ta yamma, Agatu, Logo, Apa, Otukpo, Ohimini, Obi, Ado, Okpowku, Ogbadibo, Kwande da Makurdi.
Kwamishina Akingbola ya kara gano wasu munanan dabi’u dake ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar jihar da suka hada da lalata manyan muhimman kayayyakin more rayuwa musamman safarar jiragen kasa, kungiyoyin ‘yan bindiga na cikin gida,’ yan kungiyar asiri, garkuwa da mutane, fashi da makami, kalubalen jin kai, rikice rikicen gama gari da fataucin muggan makamai.
“Matakan da suka yi daidai da manufofin gudanarwa na Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, sun haɗa da haɗin kai mai kyau da haɗin gwiwar al’umma, kamfen na jama’a da bayar da shawarwari,da aikin leken asiri ya jagoranci aikin.”
Kwamishinan ya lissafa wasu nasarorin daya samu tun lokacin daya shiga ofis ya hada da ceto wanda aka sace, kamawa da mutuwar wasu mutane biyu da ake zargi masu garkuwa da mutane, kamun wadanda ake zargi da fashi, kamun barayin jirgin kasa da kuma dawo da silifan jirgin kasa.sannan ya bayyana cewa, an cafke wadanda ake zargin ‘yan fashi da makami ne da ‘yan kungiyar asiri, sannan an kuma kwato bindigogi da alburusai daga hannun su.