Aƙalla mutum goma ne suka rasa ransu sakamakon wani sabon faɗa da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma a kudancin ƙasar Chadi.
Wani mai shigar da ƙara a yankin Moundou, birni na biyu mafi girma a ƙasar, Brahim Ali Kolla ya ce galibin kashe-kashen sun faru ne yayin gudanar da jana’iza.
Ya shaida wa kamfanin dillacin labaru na AFP cewa rikicin ya fara ne lokacin da makiyaya suka yi zargin wata saniyarsu ta ɓata kuma suka bi diddigi suka gano cewa wata gona na da sa hannu wajen ɓatarta.
Ko da suka tura wakili domin ya dawo da ita sai aka kashe shi, sannan manoman suka biyo makiyayan tare da hallaka su yayin gudanar da jana’izar mamacin.
https://dimokuradiyya.com.ng/sudan-za-ta-rage-darajar-kuɗinta/
Rikici da arangama tsakanin manoma da makiyaya masu yawo na ƙara ƙamari a yankin Sahel inda aka yawan taƙaddama kan filaye.
Mai shigar da ƙarar ya ce ko a ranar Alhamis sai da jimillar mutum 10, dukkansu makiyaya suka rasa ransu a garin na Moundou.
Sai dai ya ce tuni aka cafke mutum 43 bisa zargin su da hannu wajen tayar da rikicin, ciki har da dagattai.
Ko a ranar Litinin sai da wani rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar makiyaya uku da manoma takwas a wata arangama a kudancin kasar.