Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na fuskantar matsananciyar matsin lamba daga magoya bayansa biyo bayan rahotannin da ke cewa ya ki amincewa da bukatar gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike na tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu.
An tattaro a Abuja, a ranar Juma’ar nan cewa, an cimma yarjejeniyoyin da dama bayan ganawar ido da ido tsakanin Atiku da Wike a Landan. Wani bangare na yarjejeniyar dai an gano shi ne cewa a baiwa Ayu damar sauka mai martaba tare da ba shi masauki a sabuwar gwamnatin PDP idan an kafa ta.
Hakazalika tsaginWike ya zayyana alƙawarin Atiku na a ba shi wanda zai maye gurbin Ayu kuma mutumin ya kasance daga shiyyar Kudu maso yamma.
Karanta kuma: Yadda Tattaunawar Tinubu Da Wike A London Ya Kawo Cikas Ga PDP Da Atiku
Sai dai ba a san ko Atiku ya amince da bukatar da sansanin Wike ya yi na yin wa’adi daya ba don ba da damar mulki ya koma kudu domin gujewa cin amanar ‘yan kudu.
Tsagi Wike wacce ta zarce sansanin Atiku biyu zuwa daya a taron na Landan ta kuma samu damar fitar da wani alkawari daga dan takarar PDP na samar da shugaban majalisar dattawa da wasu manyan jami’an majalisar dokokin kasar.
Za a kuma nada mambobin sansanin Wike a cikin manyan mukamai na ministoci da har yanzu ba a amince da su ba da kuma shugabannin hukumomin tarayya da ma’aikatun tarayya idan sun ci zaben 2023.
A sakamakon haka, sansanin Wike ya amince da taka muhimmiyar rawa wajen tallata tikitin Atiku da Okowa da kuma samar da dabaru don yakin neman zabe.
Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin da ta shaida wa jaridar Vanguard a ranar Asabar, ta ce, “An kuma amince da cewa ya kamata a daina cece-kuce a kafafen yada labarai kuma wannan ne ya sa ofishin yada labaran Ariku ya dauki nayin furicin da ya yi daukar nauyin fitar da bayani a ranar Alhamis.
“An bar Atiku a daki domin tattaunawa, ya fi shi yawa mabiya kuma budaddiyar bukatar ‘yan takarar jam’iyyar Labour Party da APC, Mista Peter Obi da Asiwaju Ahmed Tinubu bai taimaka ba.”
A wani labarin kuma: Abinda Muka Tattauna da Tinubu, Atiku Da Obi a Landan, Gwamna Wike
A kwanakin baya ne gwamnan ya gana da manyan ‘yan siyasar kasar da suka hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu; dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar; da takwaransu na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da dai sauransu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Matakin da Wike ya dauka na baya-bayan nan, ya biyo bayan barazanar ficewar sa daga jam’iyyar PDP bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa da ya sha kaye a hannun Atiku, ya jawo cece-ku-ce a tsakanin jama’a amma gwamnan ya ce tuntubar da yake yi na nuna albishir ga Najeriya.