Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyiochia Ayu, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi murabus.
Ya ce bai yi murabus ba kuma ba shi da wani shiri na yin hakan a nan gaba.
Hakan na kunshe ne a wani sako da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Simon Imobo-Tswam, ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce, “Shugaban PDP na kasa, Dr. Iyiochia Ayu, bai yi murabus ba, kuma ba shi da shirin yin murabus ko anan gaba.
Da Dumi-Dumi: Ma’aikatan Wutar Lantarki Za Su Shiga Yajin Aiki
“Domin a fayyace jita-jita kan lamarin da kuma ba da muhimmanci kan mukamin nasa, an zabe shi na tsawon shekaru hudu ne” inji sanarwar.
A wani labari kuma na daban.
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 300 da kayayyakin abinci a Sokoto
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 350 da kayan abinci a wasu unguwanni uku da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abubakar Ghani, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane da dama sun rasa matsuguni a yankin.
Ya ce lamarin ya faru ne a karshen mako, inda ya ce kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Shiyar Ajiya, Makers da kuma Runji.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman Aminu Tambuwal wanda shine shugaban hukumar Alhaji Zabairu Magaji yace gidaje 250 ne suka lalata a kauyukan uku.
Ya yi nuni da cewa, ba a samu asarar rai ba a lokacin ifti’la’in amma ambaliyar ruwan ta tafi da kayan abinci da dama.
Ya jajanta wa al’ummar yankin tare da ba su tabbacin gwamnatin jihar za ta samar musu da kayayyakin agaji cikin gaggawa.
Mataimakin shugaban karamar hukumar, Ibrahim Lawal, ya yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta gano mutanen da lamarin ya shafa a cikin kankanin lokaci.
Ya kuma yi kira da a samar da kayan agaji a kan lokaci ga wadanda abin ya shafa, inda kuma ya kara da cewa, da yawa daga cikinsu sun rasa matsuguni ba tare da abincin da za su ci ba.