Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya mayar da martani game da ci gaba da rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP.
Sani ya ce murabus din Walid Jibrin a matsayin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, BoT, shugaban, ya bude sabuwar kofar rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: PDP Ta Nada Wabara A Matsayin Sabon Shugaban BoT Na Jam’iyyar
Ya bukaci jam’iyyar PDP da ta tashi tsaye wajen kawar da rikicin ta hada kai.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, tsohon dan majalisar ya yi gargadin cewa rashin hadin kai zai kai ga halakar PDP.
Ya rubuta: “Rikicin cikin gida na PDP yana kara fadada ta hanyar tsoma baki daga waje, amma wani bangare ne na wasa.”
“Ya kamata jam’iyyar ta tashi tsaye da wannan, ta hada kai, ta samu mulki domin madadin wannan shi ne kisan kai, murabus din shugaban Bot, Sanata Walid Jibrin ya bude wata sabuwar taga.”
A ranar Alhamis ne rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya dauki wani sabon salo yayin da Jibrin ya yi murabus daga mukaminsa.
Hakan ya biyo bayan rikicin da ake zargin karkata akalar wasu muhimman mukamai na jam’iyyar na kasa domin baiwa masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa.
Idan zaku iya tunawa dai shi ne babban jigon rigimar da ta kunno kai a jam’iyyar jim kadan bayan fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa.
Sai dai Jibrin ya bayyana haka ne a taron majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa da ke gudana a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Da yake nuna fusata a kan murabus dinsa, Gwamna Nyesom Wike ya bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da ya yi murabus a maimakon haka.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Kwamitin Gudanarwar Jam’iyar PDP Na Kada Kuri’a Kan Matsayin Ayu
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP da ke gudanar da taronsa karo na 97 na kada kuri’ar amincewa da shugaban jam’iyar na kasa wato Dr Iyorchia Ayu.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Ndudi Elumelu ne ya gabatar da kudirin da kuma Ishola Balogun Fulani daga jihar Kwara.