Shugaban jam’iyar PDP na kasa Uche Secondus da Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na wata kana war sirri a yau Alhamis, a garin Abeokuta dake jihar Ogun.
Secondus ya isa wani gidan Obasanjo ne dake yankin Oke Mosan na garin Abeokuta, tare da mukarraban shi, da musalin karfe 12:19 na rana.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, gana war Shugaban jam’iyar, ba zai wuce kan rikicin cikin gida da ake samu a Jam’iyar ba, wacce ke kokarin lashe kujeran Shugaban jam’iyar.
Rikicin ya samo asali ne tun a makonni biyun da suka gabata, bayan da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyar suka aje mukamin su, kuma wasu daga cikin majalissar gudanar war jam’iyar, suka bukaci ya yi murabus.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari na ganawa da hafsoshin tsaro
Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, wasu manyan mutane a Jam’iyar, sun shiga tsakanin bangarorin biyu.
Kazalika bayan zaman tattuna war, Jagororin jam’iyar ta PDP sun amince da jam’iyar ta gudanar da Babban taron ta na kasa, a watan Octoban shekarar nan, domin zabar sabbin Shuwagabanni.