Tawagar Atiku Abubakar ta gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal ranar Juma’ar nan.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, An gudanar da taron ne a sirri a gidan Wike na musamman.
Bangarorin biyu sun gana ne bayan tawagar Atiku ta gana da sansanin Wike a ranar Juma’ar, kuma ganawar dukka ta sirri.
Ganawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ana kyautata zaton wani bangare ne na kokarin sasanta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da Wike.
Wadanda Harin Jirgin Kasa Ya Ritsa Da Su, Wasu Sun Kara Samin ‘Yanci
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wakilan tsagin Atiku sun hada da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri; Honarabul Adamu Waziri da tsohon dan takarar gwamnan Ondo, Eyitayo Jegede.
Wadanda ke cikin tsagin Gwamna Wike sun hada da tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Mohammed Bello Adoki; Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia; tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke; tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko da tsohon gwamnan jihar Gombe, Dr. Ibrahim Dankwambo.
Gwamna Fintiri bayan taron ya bayyana fatan kwamitin nasa zai samu nasarar samun zaman lafiya da hadin kan da ake bukata a jam’iyyar.
Har ila yau, Mimiko, a kan tsagin na Wike, ya ce akwai bukatar a gudanar da tattaunawa don magance wasu batutuwa.
Wike ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar a hannun Atiku a watan Mayu kuma an ki ba shi mukamin mataimakin dan takarar shugaban kasa.
Gwamnan Ribas ya zargi Atiku da yin karya don bata masa suna, duk da cewa ya sha alwashin ci gaba da zama a PDP, an gan shi yana ganawa da ’yan siyasa daga jam’iyyar mai mulki ta APC da ta hamayya ta Labour Party.