Rikicin PDP: Wike ya yi barazanar yi wa makiyansa bulala a 2023
Yayin da rikicin cikin gida na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da yin ƙamari Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai yi wa makiyan sa na siyasa bulala mai ‘bakono’ a zaben 2023 mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sowore Ya Bayyana Yadda Ya Taimaki Peter Obi Wajen Samun Takara A LP
Ya ce ba zai taba barin wani abu ga Allah ba.
Wike ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shawarar da Gwamna Okezie Ikpeazu ya ba shi na ya bar duk wasu kura-kurai da ake yi masa na siyasa don Allah a lokacin da yake gudanar da wani aiki a jihar a Umuahia, babban birnin jihar Abia.
Idan dai za a iya tunawa Wike ya yi takun-saka da shugabancin jam’iyyar PDP na kasa bayan gazawar sa na neman shugabancin kasar.
Ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP amma ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda a yanzu shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Amma na karshe da ya karya bayan rakumi shi ne zaben bai daya da Atiku ya yi na Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa ba tare da la’akari da shawarar da Wike ya bayar a matsayin mataimakinsa da kwamitin zaben PDP na musamman ya bayar.
Sakamakon cece-kuce da yunkurin sasantawa da ya ci tura, rashin jituwar na barazana ga hadin kan jam’iyyar PDP gabanin babban zaben da za a yi a watan Fabrairun badi.
Wike ya bayyana bukatarsa na sasantawa, daga ciki har da tsige shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu, amma hakan yana da wuya a bi.
A kan haka ne Wike ya ki ya sauya sheka ya nace, “Allah ya ba ni abin da ya kamata in murkushe makiyana, zan yi musu bulala da barkono.”
A wani labarin kuma:Tsaro: Yadda Yan Bindiga Sukan Tare Hanyar Birnin Gwari/Funtua
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare babbar hanyar Birnin Gwari/Funtua, sun kashe wani direba tare da yin garkuwa da matafiya da dama.
Daily Post ta rawaito cewa Wani mazaunin yankin, Alhaji Ibrahim Yusuf ne ya tabbatar da hakan a yammacin ranar Litinin din nan.