Magoya bayan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun fice daga kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba matsin lamba ga Shugaban Jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da ya sauka daga mukamin.
A yayin da ake matsa wa Ayu lamba kan ya sauka daga mulki, Walid Jibrin, ya ajiye mukaminsa na shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar adawar, amma tsagin Wike ya yi watsi da hakan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A makon da ya gabata lokacin da Atiku ya ziyarci Oyo domin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, Gwamna Seyi Makinde, wanda ke da alaka da Wike, ya sake jaddada kiran Ayu da ya sauka daga mulki.
Hakan dai ya raba kan masu ruwa da tsaki a yankin Kudu maso Yamma yayin da akasarin masu ruwa da tsaki suka yi layi a bayan Shugaban PDP na kasa wanda a halin yanzu baya kasar.
Da suka tashi daga wani taro a Fatakwal da safiyar Laraba, masu biyayya ga Wike sun sha alwashin ba za su shiga ayyukan yakin neman zaben Atiku ba har sai Ayu ya yi murabus.
Cif Olabode George, wanda ya fice daga taron da aka sanar da murabus din Jibrin, ya karanta sanarwar a madadin kungiyar.
“Jerin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da aka wallafa, batun da ya dace shi ne shugabancin Ayu. Don haka mun yanke shawarar cewa Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin shugaban riko na yankin kudancin Najeriya. Mun kuduri aniyar cewa ba za mu shiga kwamitin yakin neman zabe ta kowace irin matsayi ba har sai Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus,” inji shi.
KARANTA KUMA: Wike: Ni Ba Kamar Yahaya Bello Be Ne
Daga cikin wadanda suka halarci taron da aka gudanar a gidan Wike a Fatakwal akwai tsohon Gwamna Olusegun Mimiko, Ibrahim Dankwambo, Jonah Jang, Ayo Fayose da Donald Duke.
Haka kuma akwai tsohon ministan shari’a, Mohammed Adoke; Farfesa Jerry Gana, tsohon ministan yada labarai; Shugaban Jam’iyyar PDP na Kudu-maso-Kudu, Dan Orbih; da tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Chibudom Nwuche.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Da yawa daga cikin wadanda suka halarci taron mambobin kwamitin yakin neman zabe ne sama da mutum 300 na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP.
A ranar Litinin ne Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da su magance korafe-korafen Wike, inda ya ce korar shi zai nuna hadari ga jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Za a fara yakin neman zaben 2023 daidai mako guda daga yanzu.
A wani labarin kuma: Gwamna Ganduje Ya Ɗaga Darajar Asibitin Masarautar Rano
Gwamnatin jihar Kano ta daga dajarar asibitin garin Rano zuwa asibitin kwararru mai dauke da gadaje dari hudu.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shine ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata, yayin da yake jawabi a wurin taron bikin kaddamar da asibitin da aka gudanar a harabar sa a cikin garin Rano.