Kananan yara 97 ne ‘yan kasar Ukraine suka mutu tun farkon mamayar Rasha a kasar, yayin da ake ci gaba da gwabza fada, inji shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaba Zelensky ya bayyana hakanne a yau talata a wani jawabi ga majalisar dokokin Canada.
“Sun riga sun kashe yara ‘yan kasar Ukraine 97,” in ji Zelensky a cikin wani Faifan bidiyo, ya kara da cewa sojojin Rasha suna “lalata komai: wuraren tarihi, makarantu, asibitoci, rukunin gidaje.”
“Ba mu nema da yawa. Muna neman adalci, don samun goyon baya na gaske, wanda zai taimaka mana mu yi nasara, mu kare kanmu, don ceton rayuka,” in ji shi.
Kazalika shugaba Volodymyr Zelensky ya samu yabo daga ‘yan majalisar.