Rikicin Takara Gwamnan Adamawa A APC: Kotu Ta Tsayar Da Hukunci Kan Nuhu Ribadu Da Yake Yiwa Binani
Babbar Kotun Tarayya da ke Yola ta tsayar da hukunci kan ƙarar da Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), Nuhu Ribadu ya shigar a kan APC, da Ƴar Takarar Gwamna a Jihar Adamawa, Aishatu Ahmed Binani.

KARANTA WANNAN LABARIN: Na taɓa yin aikin gadi – Mawaƙi D’banj
Nuhu Ribaɗu wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar APC ya sha kaye, inda ya garzaya kotu da neman a soke nasarar Binani.
A ranar Laraba ne babbar Kotun Tarayya da ke Yola ta tsaida ƙarar domin yanke hukunci nan gaba kaɗan.
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Abdulazeez Anka, ya ce za a sanar da ranar da za a yanke hukunci ga ɓangarorin da abin ya shafa.
DAILY POST ta gano cewa a zaɓen fidda gwani na Gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a Yola a ranar 27 ga watan Mayun 2022, Binani ta samu ƙuri’u 430, inda Nuhu Ribaɗu ya samu ƙuri’u 288.
Sauran ƴan takara huɗu da suka samu ƙuri’u, dukkanin su da aka hada sun kama ƙuri’u biyu ne fiye da wakilan da aka amince da su.
Kwamitin da ya gudanar da zaɓen Fidda Gwanin ya ce ba a tantance wakilai biyar da suka fito daga wata karamar hukumar ba, kuma a gaskiya sakamakon kuri’u uku bai kai yadda ake zato ba, sai dai wakilin Ribadu ya dage cewa an yi wasa, kuma Ribadu ya bi diddigin lamarin tare da shigar da ƙara.