By Abbas Yakubu Yaura
Kasar Syria a ranar Talata ta bayyana cewa tana goyon bayan matakin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin na amincewa da jamhuriyar Ukraine guda biyu da suka balle a matsayin masu cin gashin kansu.
Faisal Mikdad ya ce “Syriya na goyon bayan shawarar da shugaba Putin ya yanke na amincewa da jamhuriyar Luhansk da Donetsk kuma za ta ba su hadin kai.”
Kamfanin dillancin labaran kasar Syria ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Mikdad yana fadar haka a taron Valdai Forum da ke birnin Moscow a jiya Talata.
“Abin da kasashen Yamma ke yi a kan Rasha a yau ya yi daidai da abin da suka yi wa Siriya a lokacin yakin ta’addanci,” in ji shi.
Kasar Rasha dai ita ce babbar kawar shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad tun bayan barkewar yakin kasar Siriya a shekara ta 2011.
A jiya litinin, Putin ya sanar da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnati Olaf Scholz na Jamus a wata tattaunawa ta wayar tarho game da matakin da ya dauka na rattaba hannu kan takardar amincewa da ‘yancin cin gashin kai na jamhuriyar biyu masu goyon bayan Rasha.
Jamhuriyoyin biyu masu goyon bayan Rasha sun hada da yankin gabashin Ukraine da ake kira yankin Donbas.
Mikdad ya ce, Amurka da kasashen yammacin duniya na ci gaba da taimakawa ta’addanci a kasar Siriya, wanda ke barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
dpa