By Abbas Yakubu Yaura
A daren jiya ne gwamnatin jihar Ogun ta karyata rade-radin cewa Sarkin Hausawa na Abeokuta, Ibrahim Hassan Hassan ya rasu.
An samu tashin hankali a ranar Litinin 7 ga watan Maris a babbar kasuwar Lafenwa da ke Abeokuta lokacin da wasu ‘yan kabilar Yarbawa da Hausawa suka yi arangama, wanda ya yi sanadin jikkata da dama tare da kona shaguna inda Sarkin ya samu raunuka a arangamar.
Wakilinmu ya rawaito cewa an kama mutane akalla 15 da ake zargi da hannu a cikin rikicin.
Sai dai al’amura sun koma kamar yadda ‘yan kasuwa daga bangarorin biyu ke kirga asarar da suka yi.
Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Laraba an yi tashin hankali a kewayen Lafenwa da Sabo yayin da ake ta yada jita-jitar mutuwar Sarki.Inda ‘’yan kasuwa saboda tsoro da kuma fargaba suka kulle shagunansu.
Mahmmud Alhasan Tama, wanda yana daya daga cikin masu kula da Sarki a cibiyar lafiya ta tarayya da ke Abeokuta inda aka kwantar da shi, ya kuma tabbatar wa Jaridar Daily Trust cewa yana raye.
Ya ce, “Babu asarar rai; an zaci ya mutu amma bai mutu ba. Gwamnatin jihar Ogun ta dauki nauyin biyan kudin asibiti na duk wadanda abin ya shafa.
Tama ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Ogun karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Alhaji Salis Shuaib, ta ziyarci wadanda lamarin ya shafa tare da ba su tabbacin goyon bayan gwamnati kan kulawar da suke yi tare da bayar da tabbacin tabbatar da zaman lafiya a jihar Ogun.”
Shima mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Ogun kan harkokin kabilanci, Malam Hadi Sani ya jaddada kudirin Gwamna Dapo Abiodun na karfafa zaman lafiya a jihar.