Jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kabilu da addinai a Nijeriya.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a yayin zaman makoki a rana ta takwas na Marigayi Alhaji Lateef Jakande, gwamnan jihar Legas na farko na farar hula.
Tinubu ya ce; kasarnan na fuskantar rikice-rikice, wanda ya ce abin da ake bukata a yanzu shi ne fahimtar juna domin bai wa zaman lafiya damar dorewa.
Tinubu ya ce kowa ya yi hakuri a zauna lafiya, saboda a cewarsa bamu da kasar da ta wuce Nijeriya; “idan akwai rikici, ina zamu je? Zamu cika dukkanin yammacin Afrika ne, babu inda zai iya daukarmu”, ya tabbatar.
Tinubu ya ce duk wanda ya taba ganin abin da yaki ke haddasawa, ba zai taba sha’awar rikici ba, kuma ba zai taba son Nijeriya ta fada irin wannan rikicin ba.