Tsohon dan wasan Manchester United da Ingila Rio Ferdinand ya ce lokaci ya yi da ya kamata a ce kasar ta baiwa dan wasan ta Jadon Sancho damar fafata wasa a gasar Euro 2020 dake gudana yanzu haka.
Dan wasan mai shekara 21 ya gaza samun kansa cikin jerin yan wasan kasar da suka doke Croatia 1:0, kazalika haka zancen yake a wasan da kasar ta yi kunnen doki da Scotland a ranar Juma’a.
Kasar Ingila jimilla tun fara wannan gasa ba ta yi bugun da ya nufi raga da ya wuce uku ba, wannan ya sa ake ganin rashin samun jajirtaccen dan wasan gaba ne.
“Ina da tabbacin cewa muna da yan wasa da suke da damar sauya wasanni a gaba, kuma su yi amfani da damar su, amma kuma ba a saka Sancho” cewar Ferdinand.
Shi dai Sancho ya nuna kwazonsa a wasanni da dama a kakanni uku a Ƙungiyarsa ta Dortmun inda ya samu damar bada gudunmawa a kwallaye 109 cikin wasanni 106 da ya fafata.