Za a iya cewa ritayar dole ta tabbata akan shahararren ɗan tseren kekennan daya saba lashe lambar yabo a duniyar masu gudanar da tseren keke wato Ineos Granediers.
Ritayar ta tabbata ne biyo bayan mummunan rauni daya samu wanda koda yaci gaba da yin gasar bazai barshi ya dinga lashe lambobin yabo ba duba da cewar a maƙarfafarsa yake wato ciwon da yaji kenan.
Shidai wannan shahararren ɗan tseren keke ya saba zuwa matsayi na 1 a kusan dukkanin gasar da zai fafata. Dangane da hakanne likitoci suka bashi shawarar kawai ya haƙura ya jingine wasan tseren keken kawai idan har yanason ya tsira da lafiyarsa.
Gasar tseren keke dai itama tana daga cikin gasar motsa jiki kuma anayin gudu na gwaninta da kuma bajinta sosai da sosai wajen gudanar da tseren idan ana fafata shi.