By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas tace ta bayar da umarnin rusa dukkanin sansanonin da ake tsare da haramtattun kayayyakin da wata kungiyar ‘yan banga mai suna OSPAC ke gudanar dasu a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Fatakwal, babban birnin jihar.
Omoni yace kwamishinan ‘yan sandan jihar, Friday Eboka ne ya bayar da wannan umarni a wata ganawa da yayi da dukkan jami’an ‘yan sanda na shiyya da kwamandojin yankin a jihar.
Yace rundunar ‘yan sandan ta kara zage damtse wajen cafke wani kwamandan kungiyar ‘yan banga da ake nema ruwa a jallo a Elele, karamar hukumar Emuoha ta jihar, mai suna Fucking Naira.
An dai gurfanar da wanda ake nema ruwa a jallo bisa bacewar wani matashi dan shekara 17 mai suna Chibuike Nwokedi, dalibin SS1 na makarantar sakandare ta Jesus Our Savior International dake Elele.
Sannan yace, “Kwamishanan ‘yan sandan bai dauki abin da wasa ba. A ranar Alhamis din data gabata, CP ya yi wata ganawa da dukkan DPOs da kwamandojin yankin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Omoni yace dole ne a rusa dukkan sansanonin OSPAC kuma ’yan banga zasu yi aiki a karkashin kulawar DPOs da kwamandojin yankin.”
“Muna yin iyakacin kokarinmu kuma shi ya sa muke daukar wadannan matakan. Kalaman da mutanen da aka kama aka kai su kotu, duk sun nuna cewa sun mika shi ga Kwamandan OSPAC, wato Fucking Naira,” inji shi.