Hukumar dake yaki fa yi wa tattalin arzikin kasa zagon Kasa EFCC ta cik hannu da tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha.
Rahotanni sun bayyana cewa a yau talata ne hukumar ta yi ram da Okorocha a birnin tarayya Abuja bisa zargin shi da wadaka da dukiyar al’umma daga lokacin mulkin sa a shekara ta 2011 zuwa 2019, zargi da Okorocha ya hau teburin naƙi.
Idan za a iya tunawa Gwamnan Jihar Imon a yanzu Hope Uzodinma ya rarike wsu daga kadarorin nai dakin Okorocha bisa zargin cewa ta mallake su ne ba bisa ka’ida ba.
A watan Fabrairu an ga Okorocha a Ofishin Yan Sanda inda aka ce ya je ne kare dukiyar matar tashi da aka rarike.
Wannan Kamu da EFCC ta yi shine babban kamu da ta yi karkashin sabon shugaban ta Abdulrasheed Bawa, to sai dai daga bisani an saki Okorocha ya kama gaban sa.