Sanata Rochas Okorocha ya kalubalanci gwamnonin yankin Arewa da cewa basu yi wa tsarin karatun almajiranci adalci ba.
“A taimake su a basu ilimi, a basu ayyukan yi, saboda ba wanda yasan me gobe zata yi, watakila a samu shugaban kasa a cikinsu”
Okorocha yayi wannan jawabi ne a yayin wata tattaunawarsa da BBC.
Tsohon gwamnan Imo Okorocha yace “kamata ya yi a taimaki tsarin a masa garanbawul, gwamnoni da masu kudi su shiga cikin tsari ba wai suke wulakanta shi ba, saboda da yawa daga cikin shugabanninmu a yanzu duk sun yi almajiranci”.
https://dimokuradiyya.com.ng/sai-mun-kawo-karshen-almajirci-a-arewa-el-rufai/
Ya kara da cewa tsarin karatun almajiranci ba shi matsalar ba, matsalar ita ce yunwa da bakin talauci da ake fama da shi.
“Tsarin ya samo asali ne daga Annabi Muhammad (S.A.W) lokacin da yayi hijira kuma aka samu wanda suka bisa domin samun ilimi, sun samu kulawa tare sa ciyar da su”.
“Da yawa daga cikinmu muna da halin gyara tsarin tare da taimakawa, saboda yaran nan yaranmu ne”.
Yace gidauniyarsa ta Okorocha da ya kafa a Kano, Yola, Sokoto da Zaria zata taimakawa Almajirai.
A kwanakin da suka gabata ne gwamnonin arewa suka kafa dokar hana yin bara a yankin na arewa, kuma suka amfani da yanayin da ake ciki na annobar sarke numfashi inda maida Almajiran garuruwansu.