Bayan daukar tsawon lokaci ana tsumayar fadowarta, daga karshe dai mashahuriyar rokar nan ta kasar China ta fado wannan duniya tamu.
Ɓurbushin rokar da tun usuli dama tun an harba ne a watan da ya gabata, a yanzu haka ta faɗa a Katafaren tekun Fasha dake Indiya kamar yadda Hukumar dake kula da sararin Subuhana ta Kasar ta bayyana.
Mahukunta a kasar china sun ce burbushin rokar ya yi ta’adi matuka, to amma dai bisa izni na Ubangiji bai taɓa rai da lafiyar bil’adama ba.
Kafar watsa labaran China ta ruwaito cewa rokar ta faɗa a wani tsibiri na Indiya inda ke da nisan murabba’in degiri 72.47 a ɓangaren gabashi, yayin da a arewaci kuma bai fi digiri 2.65 ba.
Ko da yake an ce ta faɗa ne a yammacin Maldives, to amma Hukumar Kula da Sararin Subuhana ta Kasar Amurka ta ce ba ta san takamaiman ina ne ta afka ba.
Da ma tun da farko kasar Amurika da kuma ƙasashen yamma sun ce suna hango shawagin rokar, to amma suna tsoron kakkabo ta ne saboda gudun magana.
Sa misalin karfe 10:24 agogon Beijing ne dai wato dai-dai da 2:24 kenan agogon GMT na daren Asabar wayewar garin Lahadi rokar ta yi dirar mikiya a wannan duniya tamu.
Gabannin Fadowar rokar sai da kasar Amurka ta zargi China da wasa da rayuwar jama’a bisa yadda take rikon sakainar kashi wa fadowar tata.