Cikin Kasa da wata guda kenan da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila ta kori kocin ta Jose Mourinho, amma tuni har ya sake samun sabuwar kungiya da zai ja ragamar ta.
Tottenham ta dauki matakin korar Mourinho ne bayan shafe shekara ɗaya da rabi ba tare da tabuka abin arziki ba musamman a kakar bana tun bayan karɓar aiko daga hannun Mauricio Pochetino.
To sai dai ga Kungiyar Kwallon Kafa ta Roma dake kasar Italiya, wacce Mourinho zai karbi ragamar horas da ita daga farkon kaka mai zuwa, ta ce lallai tsuntsu daga sama Allah Ya turo mata gasasshe.
Ko da yake kwanaki kadan bayan korar sa ne daga Tottenham din, shahararren kamfanin nan na TalkSPORT dake sharhin wasanni ya dauki Mourinho a matsayin mutum na gaba da zai ci gaba da bata sharhi a kan harkokin wasa.
A yanzu haka dai Roma na ta tirka-tirkar yadda za ta tsallaka zuqa gasar zakarun nahiyar turai a kaka mai zuwa ne, bayan da ta makale a mataki na shida a teburin Serie A.
Ko da yake har yanzu da sauran dama a gareta ta zuwa gasar a badi ta hanyar lashe kofin Europa, ko da yake damar kadan ne domin sa ta chasa Manchester United kwallaye hudu da haushi gabannin tsallakewa zuwa wasan karshe da zai ba ta damar lashe kofin