Dan wasa gaba na Juventus, Cristiano Ronaldo ya zura kwallo biyu a wasan sun a gasar Serie A da suka lallasa Udinese da ci 4 da 1 a filin wasa na Turin a ranar Lahadi.
Wannan nasarar da suka yi ya sanya kungiyar ta koma ta 5 a teburin gasar.
Ronaldo ya fara zura kwallon farko ne a minti na 31. A inda a initi na 49 ya ba da kwallo Federico Chiesa kuma ya zura ta.
A minti na 70 ne Ronaldo ya kara ta biyu, wanda ya maishe da wasan 3 da ba ko daya. Sai dai kuma a minti 90 Udinese suka zura daya.
Inda kuma na gab da tashi Paulo Dybala ya zura kwallo daya.
Udinese sun koma na 13 sakamakon rashin samun nasara a wasanni hudu a jere.