Kwamishinan yan sanda na jihar Legas Hakeem Odumosu ya ce, daga yau Alhamis, an haramta duk wani gaggamim na zanga-zanga a kowani irin hali a dukkannin sassan jihar.
Odumosu ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da manema Labarai a Alausa na garin Ikeja, da ke cikin jihar Legas.
Inda ya ce, rundunar ta na garkadin masu shirya zanga-zanga a jihar irin su, Sunday Igboho da Banji Akintoye da kuma magoya bayan su, da su guji hada wani gaggamin da zai sa a rufe hanyoin jihar.
Inda kuma ya yi gargadi cewa, duk wanda rundunar ta sake kama wa da karya dokar, zai fuskanci fishin hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata sabuwa: KAROTA ta ƙara kuɗin lasisin A-dai-daita sahu zuwa N100,000
Idan za’a iya tunawa dai, an sha hada wasu gaggami a Legas, wadanda su kayi sanadiyar asaran rayuka da dukiyoyin al’uma.