Sanata Rufa’i Sani Hanga ya lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hanga ya samu tikitin ne wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya janye daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP.
An gudanar da tabbatar da nadin Hanga ne a ranar Alhamis a cibiyar matasa ta Sani Abacha da ke Kano karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ta tsakiya, Abdullahi Zubair, tare da shaidar da daruruwan mabiya jam’iyyar a fadin kananan hukumomi 15 da suka hada da ‘yan majalisar dattawa.
Karanta kuma: Ina Matukar Tausayawa Shekarau Bisa Komawarsa PDP
Shekarau, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma PDP, bayan wasu rigingimu da ba a warware ba.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, sun je Kano domin karbar Shekarau.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya ce ficewar Shekarau ba zai shafi damar jam’iyyarsa a zaben 2023 ba.
A wani labarin kuma: Dole Ne Najeriya Ta Magance Matsalar Satar Danyen Mai, Inji Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace dole a magance matsalar satar danyen mai.
Ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan tattalin arzikin kasa wanda ya kaddamar a ofishinsa a ranar Juma’ar nan.