Ministar Kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed Shamsuna ta ce rufe iyakokin Nijeriya ya jawo tashin farashin kayayyaki a kasar.
Kalaman na ta na zuwa ne yayin da rahoton Hukumar Kididdiga ta Nijeriya ya ce tashin farashin kayayyaki ya kai kashi 11.61% a watan Oktoba.
Ministar ta fadi hakan ne ranar Laraba, kamar yadda rahoton Bbc Hausa ya tabbatar, inda ta ce wannan alkaluma da hukumar ta fitar suna sane da su tun a watan Satumba.
“Hauhawar farashin kaya ya sauko a cikin ‘yan watanni amma ya ci hawa a wata biyu da suka gabata, inda yanzu ya kai kashi 11.61% a karshen watan Oktoba,” in ji a Zainab Shamsuna.
Ta ci gaba da cewa: “Hauhawar da aka samu tsakanin Satumba zuwa Oktoba ya faru ne saboda tsadar kayan abinci da kayan kanti da kuma kifi.
“Daya daga cikin dalilan da ya jawo hakan shi ne rufe iyakoki. Rufewar ta dan wani lokaci ce sannan kuma karin da aka samu na kashi biyu ne kawai (a kan na baya).
“Nijeriya tana tattaunawa da makwabtanta kan batun kuma tattaunawar ta yi nisa.”
Ministar kudin kuma ta ce burin gwamnati shi ne ta kare tattalin arzikin kasa daga durkushewa idan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka maras shinge ta fara aiki.
Nijeriya dai ta saka hannu kan yarjejeniyar tun a watan Yulin 2019, wadda ta tanadi shigar da kayayyaki na kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka ba tare da shamaki ba.