Shugaba Hukumar DSS, Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Nijeriya da gwamnatin tarayya ta yi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimakawa jami’an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.
Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri a Abuja. Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.
Shugaban DSS ya yi kira ga daliban da ake yayewa su yi amfani da ilimin da suka samu a wuraren aikinsu domin taimakawa gwamnati wajen dakile matsalolin tsaro.
Za ku tuna cewa a ranar 21 ga Agusta, gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin Nojeriya hudu domin kawo karshen fasa kwauri domin inganta tattalin arzikin kasa. A cewar mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno, ba za a bude iyakokin ba har sai an cimma manufa.