Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma a ranar Laraba sun ziyarci wurin da gini mai tsawon bene 21 ya rufta a yankin Ikoyi na Jahar Lagos, inda suka jajantawa Gwamnan Jahar Babajide Sanwa-Olu.
Sakataren ƴan jarida na Sanwa-Olu Gboyega Akosile ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar.
Ƙungiyar wanda shugaban ta ya wakilta Kuma Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari da takwaran sa Abdullahi Umar Ganduje, sun yabawa Sanwa-Olu daya sanya kwamitin bincike akan ruftawar ginin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jigin Saman Nigeria Zai Fara Aiki A Sabon Watan Afurilu Mai Zuwa
Gwamnonin wanda suka samu rakiyar Sanwa-Olu zuwa wurin sun jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa a wurin da ginin ya rufta, wanda ya faru a ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.
A lokacin ziyarar, Masari yace ” mun zo ne a wannan wuri domin wakiltar Gwamnonin Arewa Maso Yamma domin jajantawa Gwamnan Lagos, iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Lagos gaba ɗaya akan wannan lamari daya faru.
“Muna addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar wannan lamari. A madadin Al’ummar Arewa maso Yamma, muna miƙa ta’aziyya da jaje.
A jawabinshi Gwamnan Lagos Sanwa-Olu ya bayyana cewar a lokacin da Gwamnati ke bakin ƙoƙarin ta wajen gano dalilin faruwar lamarin, ina farin ciki yanda manyan mu ke zuwa domin jajanta ma Gwamnati da Jama’ar Jahar Lagos.
Comments 1