Adadin wadanda suka mutu a wani bene mai hawa 21 da ya ruguje a Ikoyi da ke Legas a ranar Litinin ya tashi daga 22 zuwa 36.
Daga cikin mutuwar mutane 36 da aka samu kawo yanzu, uku mata ne yayin da sauran 33 maza ne.
Ko’odinetan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA a shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, wanda ya bada labarin ya ce, daga cikin mutane tara da aka ceto, daya mace ce, yayin da sauran takwas din kuma maza ne.
“A cikin wadanda suka tsira, muna da mace daya da namiji takwas. Daga cikin wadanda suka mutu, muna da mata uku da gawarwakin maza 33.”
“Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto kuma ƙarin mutane sun shiga tawagar aikin ceto,” in ji shi.
Ginin da ake ginawa a titin Gerrard da ke unguwar highbrow a Legas ya ruguje ne a ranar Litinin din da ta gabata, inda mai gidan da wasu ma’aikatan ginin ke karkashin baraguzan ginin.
Comments 1