Masu ceto a birnin Miami na Amurka na can na ci gaba da sansano ko da karin mutane a cikin ɓaraguzan wani bene mai hawa 12 da rufta a kasar.
Kawo yanzu dai mutum guda ne ya gamu da ajalinsa yayin da mutane 99 suka yi ɓatan dabo, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Yan uwa da iyalai na ci gaba da zura idanu don samun kyakkyawan labari, yayin da tawagar masu ceto ke ta karakaina don ganin an samu nasara.
Har kawo yanzu dai ba a gano Musababbin rugujewar benen mai shekara 40 wanda ya rufta a ranar Alhamis.
Kuma tuni shugaba Joe Biden ya yi umarnin tura jami’an agajin gaggawa don bada tallafi wajen ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.