Yayin da aka wuni na hudu da rugujewar gini a Amurka, Ma’aikatan ceto na a birnin Miami na Jihar Florida dake kasar ta Amurka na can na ci gaba da aikin ceto son gano mutane sake da sauran numfashi.
Kawo yanzu mutane 150 ne aka yi imanin cewa sun salwanta, yayin da tara kuma ake kyautata zaton sun rigau gidan gaskiya a lamarin sa ya faru ranar Alhamis.
Kuma tuni aka gano yan uwa da iyalan hudu daga mamatan, ko da yake har yanzu ba a gano Musababbin rugujewar benen mai hawa 12 na.
Sai dai wasu injiniyoyi sa aka kawo a shekarar 2018 sun tabbatar da cewa zanen ginin bai tsaya yadda ya kamata ba, lamarin da ke hana ruwa gudana a ɓangaren ginin.
A ranar Lahadi ne ma’aikatan ceto suka bayyana imanin su na samo karin mutane dake da sauran numfashi a cikin ɓaraguzan benen.
Ma’aikatan ceto daga Isra’ila da Mexico duk sun yi maja wajen ganin sun taimaka don aamun nasarar aikin ceton.