Rundunar Ƴan sanda a Kano ta bada tukuici ga Ɗan Adai-daitar da ya taimaka wajen cafke Ɓarayi
Rundunar Ƴan sandan Najeriya, ta bayar da gudummawar kuɗi ga wani Ɗan Adai-daita saboda taimaka wa, wajen Damƙe ƴan fashi da makami a jihar Kano.
Kwamishinan Ƴan Sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa kyautar kuɗin ga Ɗan Adai-daitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Naira Biliyan 900 da aka fitar domin yaƙi da Ta’addanci bai isa ba– Lawan
Ya ce an karrama Ma’aikacin Adai-dai da kudi saboda ya taimaka wa ƴan sanda wajen cafke waɗanda ake zargi da fashin wayar salula a cikin birnin Kano.
Ya ce ƴan sanda sun samu rahoton cewa ƴan fashi da makami a kan babur, sun kwace mata fasinja ta wayar salula a Gadon Kaya Quarters a kan hanyarta daga Rijiyar Lemo Quarters zuwa Sharada Quarters Kano.
A cewarsa, nan take tawagar ‘yan sandan da ke sintiri suka shiga aikin, kuma tare da taimakon ma’aikacin Babur mai Ƙafa uku an kama mutanen biyu tare da kama su.
Ya ce an gano wayar salula kirar Android da makami mai kaifi daga hannun mutanen biyu.
Kwamishinan ya ce kyautar kuɗin za ta kara karfafa gwiwar jama’a wajen tallafa wa jami’an tsaro wajen daƙile laifuka da aikata laifuka.
Ya shawarci mutanen jihar da su daina fallasa wayoyinsu da sauran kayayyaki masu daraja yayin da suke wucewa.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Ya kuma yabawa al’ummar jihar, sannan ya buƙace su da su ci gaba da baiwa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai.