Hukumomin ‘yan sanda a Ghana sun gargadi malaman addini da su auna furucinsu a lokacin sakwannin sabuwar shekara ko kuma su fuskanci hukuncin dauri na shekaru bakwai.
Rundunar ‘yan sandan Ghana ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Sanarwar Hukumar ‘Yan sandan Ghana Kan Sadarwar Annabce-annabce da kuma tasirinsu na shari’a’ sannan ta fitar da shi a ranar Litinin.
Hukumomin kasar sun ce, tsawon shekaru da dama da suka wuce, sadarwar annabce-annabce na cutarwa, da hadari, da mutuwa, da wasu malaman addini suka yi, ya haifar da tashin hankali da firgici a cikin al’ummar Ghana tare da jefa rayukan mutane da dama cikin hadarin tsaro.
Don haka, sun bukaci shugabannin addinai su kalli yadda suke isar da sakon annabce-annabce a cikin sakwannin sabuwar shekara kuma sun kara da cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci daurin shekaru biyar a gidan yari.