By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tace ta kubutar da mutane Takwas daga hannun ‘yan bindiga wadanda aka dauke su, a yankin Bagudu dake jihar.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Muhammad Shehu ya rabawa manema labarai a Gusau yau Talata.
Sanarwa ta kuma ce, Wadanda aka kubutar din, sai da jami’an ‘yan sanda su, suka binciki lafiyar su, kuma bayan sun tabbatar da kalau suke sannan suka mikawa iyayen su.
Kazalika ya bada tabbacin rundunar ‘yan sandan jihar wajen ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro, domin kubutar da wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Jami’in hulda da jama’ar ya kuma bukaci ma zauna yankunan jihar da su dinga baiwa jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro hadin kai wajen gudanar da ayyuka, da nufin samar da zaman lafiya tsaro.